Na gode.
Akwai wani sarki wajen ƙasar India.
An zarta da doka wai
dole ne duk fawada su kawo masa baiwa.
Abin da suka kawo,
ga aɗalashi, ga takuba masu kyau,
kuma ga zinariya.
Sai dukansu sun ƙare gai da sarki,
an ga wani gajeren mai-tsoho.
Ya bi hanyar teku
yana doguwar tafiya sosai.
Da ya matsa wajen sarki, ɗan sarki
ya tambaya: me ka kawo kana gaisuwa?
Mai-tsoho ya miƙe hannunsa da hankali,
sai aka hangi kyakyawan
ɓawon kifi da ya nuna misalin launin
shuni, rawaya, ja, shuɗi.
ɗan sarki ya ce,
"Wane ne irin banza!"
Mai-tsoho ya tashi kai da hankali
ya ce,
"Doguwar tafiya....baiwa ke nan."
(Dariya)
Sai an jima kaɗan, kuma zan ba ku
wani abin gaisuwa,
abin da na gaskata
dole ne kowa ya same shi.
Amma yanzu, bari mu kai ku
ga "doguwar tafiya" tawa.
Kamar yawacinku,
Na soma rai tun ni ke yaro.
Kuma wa ya soma rai
tun ya ke yaro cikinku ?
...
kaɗai rabinku dai? To...
(Dariya)
Sauranku fa?
Ku fi ƙaruwa lokacin da aka haife ku?
Wallahi ina so in ga mamarka.
To.
Magana game da "rashin yiwuwa"
Lokacin da ni ke yaro, ina yawan tunanin
in gama abin rashin yiwuwa.
Yau, shi ne ran da nake fata
shekara shekaru.
Saboda yau, shi ne
lokacin da zan yi ƙoƙarin
in yi abin rashin yiwuwa gabanku,
a nan dai, TEDxMaastricht
yanzu, a farkon lafazina,
in nuna muku ƙarshe
Kuma, zan tabbatar muku:
"Abin rashin yiwuwa, ya yiwu."
A ƙarshe, zan ba ku wannan abin gaisuwa:
zan nuna muku wai dukanku kuma
kun iya abin rashin yiwuwa.
Da na nemi hanyar rashin yiwuwa,
na iske wai
Kowa cikin duniya yana da abubuwa biyu:
Tsoro,
da mafarki.
Da na nemi hanyar rashin yiwuwa,
na iske
Akwai abubuwa 3 da suka sa
ƙaunata gare abin rashin yiwuwa:
"Dodgeball", watau "ƙwallon doke-doke",
da Superman,
da sauro,
Kalmomin muhimmanci 3 gare ni
Yanzu ku ga dalilin da ya sa
na yi abin rashin yiwuwa
Ni na kai ku cikin wannan tafiya
ga tsoro zuwa mafarki,
ga magana zuwa takobi.
ga ƙwallon doke-doke
zuwa Superman
kuma sauro.
To, Ina so in nuna muku
yadda zaku iya abin rashin yiwuwa.
4 ga watan Oktoba, shekara ta 2007,
Zuciyata ta bubbuge,
gwiwata ta yi rawa sosai
Lokacin da na zo gaban masu sauraro
a Sanders Theatre, Jami'a Harvard
Wannan lokaci, ina samu
"lambar yabo ta Ig Nobel" (Ig Nobel Prize)
na likita na shekara 2007
Don takardar bincike
da na haɗa da wani mun rubuta
Ana kiranta "Cinyen takobi
da sakamakonsa"
(Dariya)
An bugi takardar nan cikin wani mujalla,
mujalla da ban taɓa duba ba.
Mujalla ta likita wajen Ingila
(British Medical Journal)
Abin nan da ya faru, shi dai mafarki ne
bana tsammani ya yiwu.
Kuwa abin mamaki gare ni.
Girmamawa ke nan da ba zan manta ba
Amma, wannan magana bai fi tunani ba kuwa.
4 ga watan Oktoba, 1967
Ga shi, wannan
yaro maras jarumta, maras ƙarfi,
Ya sha wahalar matsoraci sosai.
Lokacin da ya zo gaban masu sauraro
Zuciyarsa ta bubbuge,
gwiwarsa ta yi rawa sosai
Ya buɗe bakinsa yana ƙoƙarin magana,
amma ba abin da ya fito daga baki
Da jikinsa yana rawa,
ya tsaye ya kuka
Ya yi kurum da cirko-cirko
da tsoro.
yaro nan maras jarumta, maras ƙarfi,
yana jin tsoro sosai.
Yana tsoron duhu.
Yana tsoron tsawo
Yana tsoron gizo da maciji.
Wa ya ke tsoron gizo da maciji cikinku?
To, waɗansu
Yana tsoron ruwa da babban kifi
Yana tsoron likita da majiyyaci
da allura da kuma mai-tsini iri-iri.
Amma, abin mafi muhimmanci,
yana tsoro:
mutane ne.
yaro nan maras jarumta, maras ƙarfi,
ni ne.
Ina tsoro lalacewar nasara
da ƙin amincewa
da rashin mutunci da sakamakonsu,
kuma, da abin da bai kasance ba
shekaru baya:
"social anxiety disorder"
watau ricike-rikicen jama'a.
Sabo da tsoro, shi ya sa a kan
yi mini dariya, a kan doke ni.
A kan kira ni da sunayen wulakanci.
A kan hana ni wasa da shi.
...
sai wasa ɗaya--
ƙwallon doke-doke.
Ni ba kyakyawar mai-doke ba ne.
Da waccan azzalumai su kira ni
sai in hangi ƙwallaye can
suka yi wuf suka buge fuskata.
Bam, bam, bam!
Ina tunawa wai ko yawan kwanaki baya,
da jar fuskata kamar an ciza,
da kumburarren kunnayena kamar an busa
da idanuna suka ciko da hawaye maƙil
da magana mai cin mutunci
ta ƙona cikin kunne.
An ce.
"abin da ya lalace ni, sanda da dutse ne,
amma ba magana ba ne."
Wallahi ƙarya kuwa!
Magana ta yi rotse kamar wuƙa.
Magana ta yi rauni kamar takobi.
Magana ta sa rauni mai zurfi
har ba a gani ba.
To, ina da tsoro.
Kuma babban magabcina, magana ce,
har yanzu.
Amma, ina da mafarki.
Abin da na ke fata:
bari in gudu wa labaran Superman,
bari in karanta littattafan Superman,
bari in zama jarumi mai girma
kamar Superman,
bari in yi yaƙi domin adalci da gaskiya,
bari in yi yaƙi da aljanai,
bari in yi shawagi in kewayen duniya,
bari in ci nasara in ceto rayuka.
Kuma, ina tunanin abin gaskiya.
Na karanta littafin na bajintar duniya da na
"Believe It or Not."
Wa ya taɓa karanta waɗanan littattafai?
Ina son su sosai!
Na ga mutane da suka gama abin mamaki.
Shi ya sa cewa nake: zan yi kuma
Idan azzalumai
su hana ni wasanni ke nan,
zan yi abin al'ajibi.
Zan yi abin mamaki wadda
azzalumai basu iya ba.
Zan bincike muhimmancina.
Zan kasantar da dalilin rayuwata.
Zan canji duniya.
Zan hakikanta wai abin rashin yiwuwa
ya yiwu dai.
Shekaru 10 da suka wuce,
ga makon can kafin na ciko shekaru 21.
Da abubuwa 2 suka faru a lokacin guda, sai an canza mini rayuwata har abada.
Wannan lokaci, na zama a Jihar Tamil Nadu,
India ta Kudu.
Ga aikina wa'azi ne.
Wani aboki ya tambaye ni:
"Kana da 'Throme', ko?"
Na ce: "mene ne 'Throme'?"
Ya amsa: " 'Throme' shi ne
babbar manufar rayuwa,
"watau da mafarki da manufa suka haɗu.
Kamar
"ka iya komai kake so,
ka iya tafiyar ko'ina kake so,
ka iya zama kowa kake so"
Ina za ka?
Me zaka yi?
Kai wane ne?
Na ce: "Ban iya ba! Ina jin tsoro sosai!"
Da daren can, na ɗauki tabarma na hawa
rufin kan gidana,
na kwanta ƙarƙashin taurari
na yi kallon jemagun suka
kawo wa sauro sura.
duk abin da nake tunani, ga Throme,
ga mafarki, ga manufa,
kuma ga azzalumai da ƙwallon doke-doke.
Sai na tashi na iske wai
zuciyata ta bubbuge,
gwiwata ta yi rawa sosai.
Wannan lokaci, ba don tsoro ba ne.
Na ji ciwon duk jikina.
Kwana 5 mai-zuwa,
da ciwon nan ya kawo mini suma, na yi yaƙi
da shi don rayuwata.
Cizon sauro ya sa ni mugun zazzaɓin 40.5℃
kamar na ji wuta mai zafi a kaina.
Kowane lokacin da na farka,
ba abin da na tuna sai "Throme."
Tsammani nake:
"Me zan yi da rayuwata?"
To, da isowa daren nan da
na cika shekaru 21,
da hakika
na gane cewa,
waccan ƙaramin sauro,
da sunansa "Anopheles Stephensi"
waccan ƙaramin sauro
da bai fi ƙwayar gishiri girma ba
da bai fi 5mg ba,
ya dai iya kisan mutum
mai nauyi 80kg.
Na ga ita ce ta lalace ni.
Sai na gane, mai kisa ba sauro ba ne.
Ƙwayar ƙwaro da ya zama
cikin jikin sauro
shi ne mafi kisan mutane milliyoyi
kowace shekara.
Sai na gane, a'a.
watakila mai kisa ya fi ƙarami.
Amma, wannan magana ta fi girma gare ni.
Sai na gane,
abin da ya shuka mini lalacewa,
tsoro ne.
Ƙwayar ƙwaro shi ma ya
lalace mini rai.
Ka ga, akwai banbanci tsakanin
hatsari da tsoro.
Hatsari shi ya kasance.
amma tsoro shi ne aka zaɓa.
Sai na ga zaɓena:
ko nake rayuwa da tsoro sai na
mutu da kunya da daren can,
ko sai ni na kashe tsoro
na bi mafarki na zama da jarunta.
Ka ga, lokacin da ake bisa gado
ake jin mutuwa,
sai ya gane wai, fuskantarwar mutuwa
ita ma ta sa ƙauna gare rayuwa.
Abin da na iske, kowa zai mutu,
amma ba kowa ba yake rayuwa.
Ka ga, da mutuwa dai ake rayuwa.
Lokacin da aka karanto mutuwa,
sai ya karanto rayuwa.
Shi ya sa na durƙusa
canji raina zan yi.
Mutuwa bana so.
na yi ɗan addu'a na ce,
"Allah, idan ka nufe ni rai
in ciko shekara 21
"ƙoƙarin zan yi sai
tsoro bai ƙara ikon raina ba"
Kashe tsoro zan yi.
Bin mafarki zan yi.
Canji halina zan yi.
Cika raina da mamaki zan yi.
Bincika muhimmancina zan yi.
Kasantarwa wai
"abin rashin yiwuwa ya yiwu" zan yi.
Ko na tsira daga mutuwa daren can,
ku gane da kanku fa...
(Dariya)
Da daren can, na tsai da shawara
a kan Throme (manufa) 10 na farko
Zan ziyarci duk ɓangaren duniya.
da Wuraren 7 Masu-Mamaki na Duniya.
Zan koyi wasu harsuna.
Zan zama a tsibirin jeji.
Zan zama a kan jirgin teku.
Zan zama da kalibar wajen kogin Amazon.
Zan hawa dutse da ya fi tsawo
a ƙasar Sweden.
Zan yi kallon alfijir
a Dutsen Everest.
Zan shiga kasuwar waƙoƙi
a birnin Nashville.
Zan shiga ƙungiyar wasan dabbobi.
Zan yi tsalle daga jirgin sama.
A cikin shekaru 20 masu zuwa,
nasarar yawacin manufofi nake cin.
Duk lokacin da na gama ɗayansu,
na ƙara sabon 5 zuwa 10,
da Throme nawa yake ƙaruwa ke nan.
A cikin shekaru 7 masu zuwa, na zama
a kan ɗan tsibiri wajen ƙasar Bahamas.
Shekaru 7,
na zama cikin rumfa,
na kashe manyan kifaye masu kisa da mashi,
ban sa kaya ba sai ganyaye,
kuma dole ne in koyi ruwa
tare da kifi mai kisa.
Daga can na yi ƙaura zuwa ƙasar Mexico,
sa'an nan, zuwa "ƙasar kamar kwano"
na kogin Amazon wajen ƙasar Ecuador.
"Pujo Pongo Ecuador"
na zama da wata kaliba can.
da hankali, na soma samu amincewa gare
Throme da na kafa.
Na shiga kasuwa waƙoƙi
a birnin Nashville,
sai a birnin Stockholm, ƙasar Sweden,
inda na hawa Dutsen Kebnekaise.
Na koyi tabanjama,
wasa da ƙwallaye,
yawo kan tsawon sanda,
hawa keke mai wili guda, cinye wuta,
cinye madubi...
Shekara ta 1997 na ji wai
babu yawan mai cinye takobi.
Yawwa! Cinye takobi zan yi!
Na gamu da wani mai cinye takobi
na tambaye shi don shawara.
Cewa ya yi: "to, akwai shawarori 2:"
Ta farko: ya yi hatsari sosai.
ya kashe mutane masu ƙoƙari.
Ta biyu:
Kada ka yi shi kawai!
(Dariya)
To, cinye takobi ya zama wani Throme nawa.
Na aiki kan wannan fiye da sau 10
kowace rana
sai shekaru 4 suka wuce.
Idan na lasafto sau da aiki nake
sau 4 × kwana 365 × wata 12
sau 13,000 maras nasara ke nan.
Kafin na ci nasarar cinye
a shekara ta 2001,
na kafa wani Throme cewa
zan zama babban gwanin cinye takobi
cikin duniya.
Ke nan na bincike da littattafai,
da mujalloli, da jaridu,
da kowane rahoton likita.
Na koyi ilimin jikin mutane,
Na yi magana da likitoci da majiyyata.
Na sanar da duk masu cinye takobi,
Na gudanar da
Taron Masu Cinye Takobi na Duniya.
Na yi takardar bincike ta likita
game da cinye takobi da sakamakonsa.
An bugi takardar nan cikin
Mujalla ta likita wajen Ingila
(British Medical Journal)
(Dariya)
Na gode.
(Sowa)
Kuma na iske wasu abubuwan mamaki
game da cinye takobi.
Abubuwan da baku tsammani har yanzu,
amma tsmmani zaku yi bayan daren nan.
Idan ka sare naman saniya da wuƙa,
ko da takobi, tsammani zaku yi...
An ce, asalin cinye takobi
ya wuce shekaru 4000
a wajen ƙasar India,
inda wani matashi ya yi haka.
....
Tun da shekaru 150 da suka wuce,
masu cinye takobi suke amfani sosai
cikin binciken ilimin kimiyya da magani.
don ƙirƙira "madubi mai zura cikin jiki".
mai ƙirƙira sunansa Dr. Adolf Kussamaul
mutumin Jamus.
Shekara ta 1906,
an ɗauka "zanawar bugen zuciya"
don bincika rikicen cinyewa,
kuma narkewar (ta abinci cikin ciki),
da "madubi mai zura cikin jiki"
Amma, tun da shekaru 150 da suka wuce,
akwai ɗaruruwan rauni da wasu mutuwa
suka faru.
Ga shi nan, ƙandararren "madubi mai zura
cikin jiki" da Dr. Adolf Kussmaul yake ƙirƙira.
Amma an iske wai akwai mutuwa 29
tun da shekaru 150
misali wani mutumin birnin London
wanda ya soka zuciyarsa ke nan.
Kuma, akwai tsananin rauni
3 zuwa 8 kowace shekara.
Yaya na sani? Sabo da an kira ni da waya.
ga labarin 2 satin baya
ɗayansu wajen ƙasar Sweden,
ɗayansu wajen birnin Orlando.
Masu cinye takobi suke asibiti don rauni.
Ka ga ya yi hatsari sosai.
Sai ga wani abu.
Masu cinye takobi suna bukatar
shekaru 2 zuwa 10 don koyi haka.
...
Amma abin mafi mamaki shi ne:
yadda masu cinye takobi suka koyi
su gama abin rashin yiwuwa.
To, ga asiri zan ba ku ke nan:
Ku manta da abin 99.9% da bai yiwu ba.
Ku mayar da hankali kan abin 0.1% da
ya yiwu, sai ku gano yaya aka gama.
To, bari in nuna muku tsammani da mai
cinye takobi yake.
Dole ne an mai da hankali
kan tunani maimakon abubuwa.
Da hankalin daidai sarai
kamar tsinin allura,
an iya ware kayyayyakin jiki aka warware
amsoshinsu sakamakon cinye takobi,
sai ƙwaƙwalwa da tsoka
suka "koyi" tsarin nan suka "tuna"
bayan yin haka fiye da sau 10,000.
To, kuma in nuna muku yadda jiki yake
lokacin da takobi yake ciki.
Don cinye takobi,
Dole ne an zame ruwan takobi
a sama da harshe,
an tura kan ƙofar maƙogwaro
an juya takobi 90° wajen ƙashin-ƙin-cinye
zuwa tsakon maƙogwaro
sai ƙofar bututun-abinci ta sama,
an tura kan ma'amshin-motsi,
sai an zame ruwan takobi cikin
kogon-ƙirji tsakanin huhu.
Wannan lokaci,
dole ne a tura zuciya a waje kaɗan.
Idan ka yi kallo da hankali,
ka iya ganin bugen zuciya tare da takobi.
Sabo da takobi yana jinginawa kan zuciya
tsakaninsu shi ne ƙyallen-bututun-abinci kaɗai.
Abin da ka ga nan, ya kasance dai!
Sa'an nan, an zame shi sai ya
ƙashin ƙirji
ya wuce ƙofar bututun-abinci ta ƙasa,
zuwa cikin ciki,
ya tura ma'amshin-amai cikin ciki
sai hanji na farko.
da sauƙi kuwa.
(Dariya)
Idan zan wuce iyakar nan
sai bututun-Fallopian!
Jamma'a, tambayi matarka fa sai an jima...
An tambaye ni cewa,
"Jarunta kake bukata don ka ajiye
rayuwarka cikin hatsari,
ka tura zuciyarka ka cinye takobi."
Haba. Abin da yake bukatar jarunta,
shi ne: yadda yaron nan
maras jarumta, maras ƙarfi,
ya fuskance ƙi da rashin nasara
yadda ya bayyanar da zuciyarsa
ya kashe alfarma yana tawali'u
ya tsaya nan gaban yawan baƙi
ya gaya muku labarinsa game da
tsoro da mafarki
kuma, ya ajiye ransa cikin hatsari,
ba habaici ba wallahi.
Zaku gani. Na gode!
(Sowa)
Kun ga, abin mafi mamaki shi ne,
Kullum nake ƙoƙarin cika raina da mamaki
har yanzu, na gama
Amma, abin mafi mamaki,
ba cinye takuba 21 ba
...
ko ba zauna cikin ruwa mai zurfi 20ft
tare da kifaye 88 masu kisa ba
...
ba samu zafin 800℃ don zaman jarumi ba
...
...
ko ba jawo mota da takobi
don bajintar duniya ba
ko ba shiga gasa ta ƙarshe
ta America's Got Talent ba
ko ba samu lambar yabo
ta Ig Nobel ta likita ba
Haba, su ba abin mamaki ba ne.
Ko tsammanin haka mutane suke,
a'a, ba haka ba ne.
Abin mafi mamaki da gaske,
Shi ne ga yaron nan
maras jarunta, maras ƙarfi,
wanda yake tsoron tsawo,
wanda yake tsoron ruwa da kifi,
da likitoci da majiyyata
da allura da abin mai tsini
da yin managa gaban mutane,
Allah ya nufe shi ya tashi
kewayen duniya
a tsawon 30,000ft,
ya cinye takobi cikin ruwa
tare da kifi mai kisa,
ya yi magana da likitoci da majiyyata
da masu kallo a duniya.
Su ne abubuwan mamaki ke nan.
Kullum nake so in gama abin rashin yiwuwa
Na gode.
(Sowa)
Na gode.
(Sowa)
Kullum nake ƙoƙarin abin rashin yiwuwa
har yanzu, na gama
Kullum nake so in cika raina da mamaki
in canji duniya,
har yanzu, na gama.
Kullum nake so in yi shawagi kewayen
duniya kamar Superman
cece rayuka, har yanzu, na gama
Ka ga ko?
Akwai ƙaramin sashi cikin
girman mafarkin yaron nan
ya ɓoye zurfin zuciyarsa.
(Dariya) (Sowa)
Ka ga, kullum nake so neman muhimmancina.
har yanzu, na gama.
Amma,
ban gama da takobi da ƙarfina ba ne.
Kuwa na gama da "rashin-ƙarfina,"
da maganata.
Muhimmancina shi ne canji duniya,
da kashe tsoro.
Da takobi ɗai-ɗai, kalma ɗai-ɗai,
wuƙa ɗai-ɗai, rayuwa ɗai-ɗai,
in ƙarfafa wa mutane su zama jarumai,
su gama abin rashin yiwuwa da ransu.
Muhimmancina shi ne
in ba su taimakon neman nasu.
Mene ne naka?
Mene ne muhimmancinka?
Ina dalilin kake a nan?
Na gaskata dukanmu jarumai ne.
Mene ne ƙarfinka?
A cikin duniya fiye da mutane billiyan 7,
kusan babu masu cinye takobi aka bari.
...
Amma, akwai kai kaɗai ne.
ba'a kamar ka ba.
Ina labarinka?
Ina banbancinka?
Gaya labarinka,
ko da yake muryarka ba ta da ƙarfi.
Mene ne Throme naka?
Idan ka iya yin komai,
zaman kowa, tafiya ko'ina
Me zaka yi? Ina za ka?
Me zaka yi?
Me zaka yi da rayuwarka?
Mene ne mafarkinka mai girma?
Mene ne mafarkinka lokacin da kake yaro?
Ka yi tsammani.
...
Mene ne mafarkinka mafi hauka
mafi mamaki kuma mafi ɓoye?
Na tabbata magana nan ta sa
mafarkinka rashin mamaki, ko?
Mene ne takobinka?
Kowanenku ka mallaka takobi naka
takobi da bakuna biyu:
na tsoro da na mafariki
Komai ya faru,
ku je ku cinye takobinka
ku bi mafarkinka, jamma'a.
Duk lokacin da ka zama yadda kake so,
ba yauci ba ne.
Amma ga azzalumai da ƙwallon doke-doke,
ga yaran da suke shakkar iyawa
ga yaran da suke shakkar iyawarsu,
Bari in gaya musu,
"na gode."
Sabo da in ba don azzalumai ba ne,
ba za'a samu jarumai ba.
Ga ni nan ina karantarwa
abin rashin yiwuwa ya yiwu.
Wannan batu mafi hatsari ne.
Yana da kisa sosai.
Amma, ina fata zaku ji daɗi.
(Dariya)
Ina bukatar taimakonku.
(biyu, uku...)
Haba! Ina bukatar taimakon dukanku
kan ƙidayawa!
(Dariya)
Ku san magana nan ko? To?
Ku bi na mana. Ku shirya?
ɗaya,
biyu,
uku!
A'a, biyu ne. Amma ku gane.
ɗaya!
biyu!
uku!
(An ji mamaki)
(Sowa)
Yawwa!
(Sowa)
Na gode!
Na gode! Na gode!
Na gode da zuciyata!
Kuwa na gode da cikina.
Na gaya muku ina nan zan gama abin
rashin yiwuwa, sai na gama yanzu.
Amma, shi ya yiwu ne.
Na yi haka kullum.
Abin rashin yiwuwa shi ne,
yaron nan maras jarunta, maras ƙarfi,
ya tsaya nan a TEDx gaban mutane
ya canji duniya da ƙalma ɗai-ɗai,
da takobi ɗai-ɗai, da rayuwa ɗai-ɗai.
Idan na ba ka sabon tunani,
idan na sa ka gaskata wai
abin rashin yiwuwa ya yiwu,
idan na sa ka gane ka iya kuwa,
to, ga aikina ya gama, ga naka ya soma.
Kada ka yanke mafarki.
Kada ka yanke amince
Na gode don kun gaskata mini.
Na gode don kun zama sashin mafarkina.
Ga abin gaisuwa nan:
Abin rashin yiwuwa,
ya yiwu.
Doguwar tafiya, baiwa ke nan.
(Sowa)
Na gode!
(Sowa)
(Sowa)
....