-
Barka da war haka. Barka da shiga darasin sakar-kasa-da-kasa, tarihi, kimiyya da tsaro. Suna na Charles (Chals)
-
Nine zan zama jagora a wannan darasi. Don haka bisimillah.
-
Wa nake tunanin ya dace da wannan darasin? jawabi shine kai,
-
Yakamata ka dauki wannan darasi. Domin kowa ma yakamata ya dauki wannan darasin
-
tufkar-aiki da muke iya tabawa mu kuma yi amfani da ita yana tare damu a kowane lokaci. A bayyane take, idan
-
kana kallon wannan darasi. Kana kallon ne bisa sakar-kasa-da-kasa. ta yaya ne
-
wadannan abubuwa suke aiki? ka sani? wannan fa ba akan bishiyoyi ya tsiro ba
-
Mutane ne suka samar da shi, tabbas ! za kuma mu yi magana ne akan abu mai zurfin bayani
-
Watakila ma abinda ya fi komai cukurkudewa a kimiyance, watakil, amma
-
baza mu yi magana ba ne ta mahangar lissafi, kuma baza muyi magana ta mahangar
-
manhajar naura mai kwakwalwa ba. Abinda nake nufi shine baza mu matsa
-
maka ba ta wannan bangaren. Za muyi magana ne akan abubuwan ban sha'awa a kimiyance, za mu
-
hadu da wadansu mutane ma su ban sha'awa, amma wannan darasi ba a zufafan ma'ana za mu koyar da shi ba, darasi ne akan
-
sauraro da fahimta da kuma zufafa tunani akan wadannan mutane wadanda suka mayar da
-
sakar-kasa-da-kasa abinda ta zama.