Wannan ba atisaye ba ne Sunana Greta Thunberg. Muna rayuwa a farkon ƙarewarmu gaba ɗaya. Yanayin mu yana ɓaci. Yara iri na suna barin makaranta don yin zanga-zanga. Amma zamu iya gyara wannan. Zaku iya gyara wannan. Domin mu tsira, mu daina amfani da makamashi, amma wannan kadai bazai isa ba. An tattauna akan mafita da yawa, amma mafitar da ke gaban mu fa? Zan bar abokina George yayi bayani. Akwai na'ura ta mamaki mai shanye carbon daga iska, bata da tsada kuma tana gina kanta. Ita ake kira ... bishiya . Bishiya misali ce a magance matsalar yanayi. Guntayen itatuwa, ciyayi rubabbu, gandundaji, fadamu, karkashin teku, ciyayin karkashin teku, murjani, su na cire carbon daga iska su rufe. Halittu makami ne da zamu iya magance yanayin mu da ya ɓaci da su. Wadannan hanyoyin amfani da halittu wajen magance matsalar yanayinmu taimaka sosai. Ya burge, ko? Amma sai dai idan mun daina tono makamashi daga kasa. Abin takaici anan ... yanzu mun fita harkar su. Muna kashe kuɗi ninki dubu akan tallafin makamashi fiye da akan wajen da ake samar da halittu. Magance yanayi ta hanyar halittu 2% kawai yake samu na dukkan kuɗaɗen da ake kashewa wajen magance ɓacin yanayi. Wannan kuɗin ku ne, harajin ku ne, da ajiyar ku. Ƙarin abin takaici, a yanzu da muka fi buƙatar halittu muna lalata su fiye da ko yaushe. Nau'ikan halittu 200 suna ƙarewa a kowace rana. Mafi yawan tsaunukan kankara na Arctic sun salwanta. Mafi yawan dabbobin dajin mu sun bace. Mafi yawan kasar noman mu ba albarka. Don haka me zamu yi? Me zaku yi? Abu ne mai sauki ... mu kare, mu sake mayarwa kuma mu dauki nauyi. Karewa. Ana yanke gandun daji a kimanin girman filin ƙwallon ƙafa 30 kowane minti daya. Dole mu kare wajen da halittu ke yin wani abu muhimmi. Mayarwa. An lalata mafi yawan duniyar mu. Amma halittu zasu iya sake tsirowa kuma muna iya taimakawa ɗaukacin halittu su dawo. Mu daina kashe kuɗi akan abubuwan da suke bata halittu mu kashe akan abinda zai taimaki halittu. Abu ne mai sauki. Karewa, mayarwa, ɗaukar nauyi. Wannan zai iya faruwa a ko ina. Mutane da yawa sun riga sun fara magancewa da halittu. Muna buƙatar yi da yawan gaske. Kuna iya shiga cikin wannan. Ku zabi mutanen da suke kare halittu. Ku yada wannan bidiyon. Ku yi magana akan wannan. A duk faɗin duniya, akwai mutane da suke ta yaƙi wajen kare halittu. Ku shiga cikinsu! Komai yana da mahimmanci. Abinda ku ka yi yana da mahimmanci.